Game da haka, kakakin ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Gao Feng ya bayyana a taron manema labaru da aka shirya a yau Alhamis cewa, idan Amurka ta yi fatali da ra'ayin yawancin kamfanoni na nuna rashin amincewa, kuma ta tsaya kan daukar matakin kara karbar haraji kan kayayyakin kasar Sin, to kasar Sin za ta mayar da martani ala tilas.
Gao ya jadadda cewa, yakin cinikayya ba zai iya warware matsaloli ba, sai dai ta hanyar yin shawarwari na zaman daidai wa daida da sahihiyar zuciya kawai za a iya warware takaddamar ciniki a tsakanin Sin da Amurka. (Bilkisu)