Kamfanin dillancin labaru na Bloomberg ya ba da rahoto cewa, bisa binciken da kungiyar cinikayya da tattalin arzikin kasar Amurka ta yi, an gano cewa, kashi 91 cikin dari na wadanda aka tambaya suna ganin cewa, harajin da kara a yanzu haka da wanda za a sanya a nan gaba za su kawo illa ga tattalin arzikin kasar Amurka.
Jaridar The New York Times ta ba da rahoto cewa, kamfanonin kasar Amurka sun bukaci gwamnatin kasar ta dakatar da karin karbar haraji kan kayayyakin da ke shigo da su daga kasar Sin.
Wadanda suka halarci taron sauraren ra'ayi na jiya, sun hada da wasu kamfanoni da kungiyoyi a wannan fannin, ciki har da kamfanin Logitech, da hukumar kula da sana'ar fasashohin sadarwa da dai sauransu. Kamfanin Fitbit dake nazari da kera agogon zamani na kasar Amurka ya bayyana cewa, kara haraji kan kayayyakin cinikayyar dake shigowa daga Sin zai kawo ill ga kwarewar kamfanin ta nazari da yin kirkire-kirkire a kasar Amurka, da kuma rage karfin takara na kamfanin, har ma zai sa kayayyakin irin wadannan na sauran kasashe za su kara samun gibi a kasuwa.
A nasa bangaren, kamfanin Dell ya bayyana cewa, ya damu sosai kan shirin ofishin wakilan cinikayyar kasar Amurka na kara karbar haraji kan kayayyaki mafi yawa da ke shigowa da su daga ketare. (Bilkisu)