Sin ta soki matsayin Amurka game da daddale kasafin kudin ta na shekarar 2019 kan dokar kiyaye tsaron kasa
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a yau 14 ga wata cewa, Sin na adawa da ra'ayin da kasar Amurka ta zartas na daddale kasafin kudin kasar na shekarar 2019 kan dokar kiyaye tsaron kasa, ba tare da yin la'akari da Sin ba, kuma Sin ta kalubalanci Amurkan da ta yi watsi da ra'ayin yakin cacar baka, da yin takara ba tare da sanya moriyar juna a ciki ba, da kuma kin kaucewa aiwatar da ayoyin dake kawo illa ga kasar Sin.
Lu Kang ya bayyana cewa, ya kamata a duba dangantaka mafi dacewa dake tsakanin Sin da Amurka, da bin ka'idar Sin daya tak, da hadaddiyar sanarwa guda 3 a tsakanin Sin da Amurka, ta yadda za a magance kawo illa ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da hadin gwiwarsu a manyan fannoni. (Zainab)