Kakakin ta yi nuni da cewa, kafin hakan, Amurka ta dauki matakai kan kayayyaki masu amfani da karfin hasken rana da Sin ta shigar kasar, wato ta kara buga musu harajin kwastam da kashi 30 cikin dari, wanda mataki ne da ya sabawa yarjejeniyar matakan kariya na kungiyar WTO. Yayin da kasar Amurka ta dauki wannan mataki, ta samar da rangwame ga kayayyaki masu amfani da karfin hasken rana da sauran makamashin da za a iya sabuntawa da kasar ta samar da kanta, matakin da ya samar da sauki ga kamfanoninta na samar da makamashi mai tsafta ta hanyar da ba ta dace ba, wanda kuma suka kawo illa ga moriyar kamfanonin Sin a wannan fanni. (Zainab)