Kamfanonin kasar Sin na samun karin kudin shiga daga ayyukan da suke yi a kasashen dake kan hanyar "Ziri Daya da Hanya Daya"
Kididdigar ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ta ce, jimilar kudin shigar kamfanonin kasar dake aiki a kasashen dake kan hanyar "Ziri Daya da Hanya Daya" ta karu da kaso 17.8 a cikin rabin farko na shekarar nan.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar, ta ce a cikin wancan lokaci, kamfanonin kasar Sin sun samu kudin shigar da ya kai dala biliyan 38.95 daga ayyukan da suke yi a kasashen dake kan hanyar "Ziri Daya da Hanya Daya", wanda ya kai kaso 53.5 na jimilar kudin shigar kasar. (Fa'iza Mustapha)