kiddigar da hukumar kula da hannayen jari ta kasar Sin ta fitar, ta ce ayyukan masu sayen hannayen jari ta bayan fage domin samun kazamar riba ya sauka da kaso 50 bisa 100 cikin rabin shekarar nan, idan aka kwatanta da bara. An samu raguwar aikata laifin ne saboda nasarorin yaki da shi da aka yi ta samu a bara.
Wani jami'in hukumar ya ce an yi nasarar magance matsalar a sassan kula da kadarori na kamfanonin inshora da kamfanonin hada-hadar hannayen jari.
Sayen hannayen jari ta bayan fage na nufin masu kula da hanayen jari su saye hannayen jari ta asusunsu na kansu, kafin cibiyoyin hada-hadar kudin da suke wa aiki, domin su sayar su samu kazamar riba bayan farashi ya tashi. (Fa'iza Msutapha)