Muhimman batutuwan da taron kolin zai mayar da hankali sun hada da rawar da kafafen yada labarai zasu taka wajen bunkasuwar BRICS, samar da bayanai, da kuma matakan da zasu kara samar da sabuwar hadin gwiwar kafofin yada labarai na mambobin kasashen BRICS.
A sakon maraba ga wakilai mahalarta taron dandalin, mashirya taron sun bayyana cewa, mahalarta taron zasu bada gudunmowa wajen kawo sauye sauye ga ayyukan da kasashen mambobin BRICS ke gudanarwa.
Kimanin kafafen yada labarai 48 daga kasashen BRICS 5 da suka hada da Brazil, Rasha, India, Sin da Afrika ta kudu, da kuma wasu kasashen Afrika da suka hada da Namibia, Zambia da Ghana, ne suke halartar taron a wannan karo.
Kafar yada labarai mai zaman kanta ta Afrika da kudu da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua suka dauki dauyin taron dandalin.