Mataimakin ministan cinikayya na kasar Sin kana mataimakin wakilin cinikayyar kasa da kasa na kasar Wang Shouwen shi ne ya jagoranci tawagar kasar ta Sin wadda ta kunshi wakilai 30 daga hukumomin gwamnati 14 da shugaban tawagar kasar Sin a hukumar ta WTO, jakada Zhang Xiangchen a wannan zama.
A cewar Wang, tun lokacin da kasar Sin ta shiga hukumar WTO a shekarar 2001, an samu gagarumin canji, amma abu guda da har yanzu bai canja ba shi ne, yadda kasar Sin ta ke kokarin bude kofa don karfafa hadin gwiwa da samun moriya tare da dukkan kasashe.
Haka kuma tun lokacin da kasar Sin ta shiga WTO, yawan hajojin da take fitarwa zuwa kasashen ketare yana karuwa da kimanin kaso 13.5 cikin 100 a duk shekara, adadin da ya ninka sau biyu a matsayin matsakaicin yawan na duniya.
Ya kuma bayyana cewa, tun bitar da ta gabata, kasar Sin ta aiwatar da canje-canje a manufofinta na cinikayya da zuba jari, baya ga daukar wasu matakai, ta kuma ci gaba da kokarin yin gyare-gyare a harkokinta na kwastan. Yanzu haka kaso 1 bisa uku na hajojin da ake shigo da su cikin kasar ana tantance su ne a wuri guda. (Ibrahim)