Bankin Merrill Lynch na Amurka ya ba da wani rahoto dake nuna cewa, manufar ciniki da Donald Trump ke dauka, na maimaita manufa maras kyau da aka dauka a shekaru 80 na karnin da ya gabata, kamar yadda Amurka ta yi fama da mawuyacin hali a yau shekaru 30 da suka gabata. Rahoton ya kara da cewa, masu saye-saye na Amurka za su shan wuya da cin tura a sakamakon yakin ciniki da Trump ya shiga.
Masanin ciniki na Merrill Lynch Ethan Harris ya yi nazarci cewa, manufar buga haraji ta shugaba Trump, da matakin mai da hankali kan gibin ciniki tsakanin bangarori biyu, sun yi daidai da manufa irin wannan da aka dauka a shekaru 80 na karni da ya gabata, musamman ma hakan ya yi kamar da manufar da aka dauka kan kasar Japan. Merrill Lynch ya bayyana cewa, ya kamata a yi koyi da darasi daga wancan lokaci da ya gabata. (Amina Xu)