Cikin sakon nasa, shugaba Xi Jinping, ya ce aikin kare muhalli ya shafi makomar bil Adama, kana yunkurin gina al'umma bisa hanyoyin kare muhalli, buri ne na bai daya na al'ummomin kasashe daban daban.
Shugaban ya kuma bukaci gamayyar kasa da kasa, su kara korkari, tare da hadin gwiwa, don samar da wani tsarin kare muhalli a duniya, gami da tabbatar da samun ci gaba mai dorewa a wurare daban daban.
Shugaba Xi Jinping, ya kuma yi imanin cewa, za a samu sakamako a tattaunawar da ake a taron mai taken "sanya kare muhalli gaban komai, da neman ciyar da tattalin arzikin gaba bisa fasahohin da ba za su gurbata muhalli ba".
A cewar shugaban na kasar Sin, kasarsa na daukar batun kare muhalli da muhimmanci sosai, kuma za ta tsaya kan manufofin raya kasa da samun ci gaba mai dorewa, ba tare da gurbata muhalli ba.(Bello Wang)