Bayan aukuwar hadarin, babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin rundunar sojin kasar Xi Jinping ya ba da wani muhimmin umurni, inda ya umarci ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, da ofisoshin jakadancin kasar Sin dake kasar Thailand da su kara himmar ganin gwamnatin kasar Thailand da hukumomin da abin ya shafa sun kara kokarin ceton wadanda suka bace, sannan su yi kokarin ba da jinya ga wadanda suka jikkata.
Shi ma firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ba da umurni, inda ya nemi a gaggauta ceton Sinawa masu yawon bude ido wadanda har yanzu ba a same su ba, a yayin da ake kokarin ba da jinya ga wadanda suka jikkata a hadarin.
Bisa umurnin shugaba Xi Jinping da firaminista Li Keqiang, ma'aikatar harkokin waje da ma'aikatar kula da harkokin sufuri da ma'aikatar kula da harkokin al'adu da na yawon bude ido na kasar Sin sun kafa da kuma tura wani rukunin aiki zuwa lardin Phuket na kasar Thailand domin daidaita wannan lamarin a wurin nan da nan. (Sanusi Chen)