Cikin jawabinsa, Xi Jinping ya bayyana cewa, aikin siyasa shi ne aikin dake kan gaba wajen neman ci gaban jam'iyyar, wanda ke da muhimmiyar alaka da makomarta. Kana, hanyar siyasa da za a bi ita ce babban burin tsarin gurguzu na kasar Sin. Sa'an nan kuma, burin " cika Shekaru 100, Guda Biyu" shi ne babbar manufar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wato na gina zaman takewar al'umma mai walwala bisa dukkan fannoni zuwa lokacin cika shekaru dari da kafuwar Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, a shekarar 2021, da kuma gina kasa mai tsarin gurguzu, wadda ta samu wadata da dimokuradiyya da wayewar kai da kuma daidaito a lokacin cika shekaru dari da kafuwar sabuwar kasar Sin, a shekarar 2049.
Haka kuma, Xi Jinping ya ce, tushen tsarin gurguzu na kasar Sin, ya na karkashin jagorancin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar, kuma ya kamata a mai da hankali kan bukatun al'ummar kasa domin karfafa aikin siyasa na jam'iyyar, da mayar da aikin tallafawa al'umma, da kuma neman goyon bayan al'umma a matsayin aiki mafi muhimmanci. Inda ya ce kamata ya yi su rika gudanar da ayyukansu tare da al'ummar kasa da daukar bukatun al'umma matsayin bukatunsu na kansu, domin la'akari da al'ummar kasa ko da yaushe. (Maryam)