Xi Jinping ya nuna cewa, wannan aiki yana da alaka sosai wajen tabbatar da tsaron kasar, da bunkasuwar al'umma, da kawo moriyar jama'a, ya kamata a maida hankali kan wannan aiki har a tabbatar da kawar da shi baki daya. Xi Jinping ya ce, kamata ya yi, a gudanar da aikin yaki da miyagun kwayoyi bisa doka, da kara karfi a wasu muhimman yankuna, da kyautata tsarin yaki da shi, da kawar da tushensa baki daya, da kuma kara horar da matasa a wannan fanni.
An bada labari cewa, a watan Disambar shekarar 1987, a babban taron MDD karo na 42 an zartas da kudurin sanya ranar 26 ga watan Yuni a matsayin ranar yaki da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa. Ranar yaki da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa na wannan shekara na kasar Sin na da taken "Kawar da miyagun kwayoyi don yin zaman rayuwa lami lafiya." (Amina)