Kwararru daga kasashe da yankuna da suka hada da Sin da Amurka da Rasha ne suke halartar taron na kwanaki uku, inda ake saran za su yi musayar ra'ayoyi kan amfani tauraron dan-Adam na zirgar-zirga da ayyukan hidima da sauran batutuwa.
Taron yana daya daga cikin manyan taruka da suka shafi tarukan harkokin zirga-zirgar tauraron dan-Adam na duniya guda uku. Tuni dai aka gudanar da taron shekara-shekara a birane Beijing, da Shanghai da kuma na shekarar 2010 da aka gudanar a birnin Guangzhou. (Ibrahim)