Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin jin kai da samar da agajin gaggawa, Mark Lowcock ya yi kira ga sassan da ba sa ga maciji da juna a Sudan ta kudu da su tsagaita bude wuta, su kuma kare ma'aikatan agaji da fararen hula.
Jami'in wanda ya yi wannan kira a jiya Laraba, bayan kammala ziyarar kwanaki biyu da ya kai kasar, ya ce sabon fadan da ya barke a kasar ya kara cusa fararen hula cikin wahala baya da dubban mutane da suka bar matsugunansu a sassan kasar daban-daban.
Lowcock wanda ya isa birnin Juba a ranar Talata, ya kuma tattauna da manyan jami'an gwamnatin kasar, da mambobin bangaren adawa na SPLA, da hukumomin agaji da kuma abokan hulda dake aiki a kasar. Kana ya ziyarci mutanen da rikicin da ya barke a garuruwan Juba da Yei da Mundu ya shafa.
Alkaluman MDD dai na nuna cewa, kimanin mutane miliyan 4.3 ne suka bar muhallansu, ciki har da sama da mutane miliyan 1.76 da ke warwatse a cikin kasar baya ga kimanin mutane miliyan 2.5 dake neman mafaka a kasashe makwabta. Kana yawan ma'aikatan agaji da aka kashe a kasar tun lokacin da fada ya barke a kasar a watan Disamban shekarar 2013 zuwa watan Mayun wannan shekara ya tasamma 101.
Rikicin kasar Sudan ta kudu wanda ya shiga shekaru biyar, ya gurgunta harkokin tattalin arzikin kasar baki daya. (Ibrahim)