Ofishin jakadancin kasar Sin dake Sudan ta Kudu, ya mika ton 1,500 na shinkafa da kwantanonin rumfuna 27 da gidajen sauro da bargona a matsayin tallafin jin kai ga kasar dake gabashin Afrika.
Jakadan kasar Sin a Sudan ta kudu He Xiangdong, ya ce kashi na uku na tallafin shinkafar, bangare ne na shinkafa ton 8,800 da kasar Sin ta yi alkawarin ba kasar dake fama da yunwa a watan Afrilun da ya gabata, domin yaki da matsanancin karancin abinci.
Ya ce, tuni aka mika sama da ton 4,000 ga gwamnatin Sudan ta Kudu, inda ake sa ran mika sauran kafin karshen shekarar nan.
A nata bangaren, shugabar hukumar ba da agaji ta Sudan ta Kudu, Martha Nyamal, ta yi alkawarin raba tallafin ga mutanen dake da tsananin bukata a fadin kasar.
Ta kuma yabawa gwamnatin Sin bisa goyon bayan da take ci gaba da ba kasar tun bayan da ta samu 'yancin kai a shekarar 2011. (Fa'iza Mustapha)