Fannin sufurin jiragen sama na ksar Sin ya samu bunkasuwa cikin sauri a 'yan shekarun da suka gabata, amma har yanzu ana hasashen fannin zai samu karin tagomashi, in ji jami'in kamfanin sufurin.
Li Jun, shugaban kungiyar sufurin jiragen saman kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin tana kokarin sauyawa daga matsayin kasa mafi girma zuwa kasa mafi karfin ci gaba a fannin sufurin jiragen sama.
Hukumar gudanarwar harkokin sufurin jiragen sama ta kasar Sin ta kiyasta samun karuwar kashi 12.5 bisa 100 a fannin sufurin jiragen saman a shekarar 2017 wanda ya kai ton-km biliyan 108.3, da kuma fashinjoji kimanin miliyan 549 da suka yi zirga zirga, wanda ya karu da kashi 12.6 bisa dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.(Ahmad Fagam)