A yayin taron, an gabatar da rahoto mai taken "yanayin bunkasuwar harkokin yawon shakatawa a duniya", inda aka bayyana cewa, a shekarar 2017 da muke ciki, yawan kudaden da aka samu ta fuskar yawon shakatawa ya kai dallar Amurka biliyan dubu 5.3, adadin da ya kai kashi 6.7 bisa dari na ma'aunin tattalin arziki na GDP. Wannan ya nuna cewa, a halin yanzu, harkokin yawon shakatawa na taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arzikin duniya. (Maryam)