Mr. Coulibaly ya bayyana hakan ne jiya Alhamis ga manema labarai, bayan ganawarsa da ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na kasar Morocco Nasser Bourita. Ya ce ra'ayoyin kasashen sun zo daya game da yadda za a magance matsalar 'yan ci rani.
Ya ce, kasashen biyu sun kuma yi imanin cewa, hadin gwiwa tsakanin kasashen da 'yan cin rani suka taso, da inda suka yada zango da wurin da suka nufa ka iya magance wannan batu dake cikin ajandar raya nahiyar.
Ya kuma yaba gagarumin rawar da kasar Moroccon ta taka wajen yayata ajandar nahiyar game da kaurar jama'a. Tun a farkon wannan watan ne dai, kasar Morocco ta karbi bakuncin taron ministocin nahiyar game da ajandar nahiyar kan kaurar jama'a, a wani bangare na tattaunawar da kasashen nahiyar ke yi na yayata daftarin ajandar nahiyar game da kaurar jama'a wanda ake saran gabatarwa yayin taron kolin kungiyar tarayyar Afirka da zai gudana a birnin Addis Ababan Habasha a wani lokaci cikin wannan wata.
A watan Maris din shekarar da ta gabata ne, sarki Mohammed VI na kasar Morocco ya shugabanci batun daidaita kaurar jama'a tsakanin kasashen kungiyar. (Ibrahim)