A yau Alhamis ne aka gudanar da cikakken zama na biyu na kwamitin ladabtarwa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 19 a nan birnin Beijing, za kuma a shafe kwanaki 3 ake tattaunawa yayin taron, inda za a tattauna yadda za a gudanar da aikin raya tsarin hallayar 'yan jam'iyyar, da batun yaki da cin hanci da rashawa.
Kwamitin ladabtarwa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, shi ne kwamitin koli na ladabtarwa na jam'iyyar, an kuma zabi mambobin kwamitin a yayin babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin. (Zainab)