Jiya Lahadi, aka rufe taron shawarwari tsakanin wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da manyan jam'iyyun kasa da kasa a birnin Beijing. Mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, kana dan majalisar gudanarwa na kasar Sin Yang Jiechi, ya halarci bikin rufe taron inda ya gabatar da jawabi.
Cikin jawabin nasa ya ce, a cikin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a bikin bude taron, ya bayyana ra'ayin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin kan karfafa dunkulewar al'ummomin kasa da kasa bisa dukkan fannoni, lamarin da ya nuna aniyar JKS wajen yin hadin gwiwa da jam'iyyun kasa da kasa domin neman bunkasuwar kasashen duniya baki daya.
Ya kara da cewa, jawabin da shugaba Xi ya yi, ya samu yabo daga bangarori daban daban, inda suka nuna amincewarsu kan babbar gudummawar da JKS ta bayar a tarihin dan Adam.
Haka kuma, a yayin bikin rufewar taron, an zartas da "Shawarar Beijing".
Kuma, bisa labarin da aka samu, an ce, wakilai kimanin 60 na jam'iyyu da kungiyoyin jam'iyyu kusan 300 daga kasashe sama da 120 ne suka halarci wannan taro. (Maryam)