Mataimakin ministan sashen tsare tsare na kwamitin tsakiyar JKS Gao Xuanmin, ya ce mahukuntan kasar Sin, sun sha alwashin maida kasar mai bin tsarin gurguzu mai cike da adalci da daidaito, inda tuni aka tsara manufofin da za su kai ga fidda al'ummar kasar miliyan 43 daga kangin talauci nan da shekarar 2020.
Mr. Gao Xuanmin, wanda ke bayyana hakan yayin wani taron karawa juna sani a birnin Cape Town na kasar Afirka ta kudu, ya kuma yiwa mahalarta taron karin haske, game da sakamakon da aka cimma yayin taron wakilan JKS karo na 19 da ya gudana a watan Oktoba.