in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna kiyayya ga ayyukan ta'addanci bisa ko wace irin manufa
2016-12-20 20:24:37 cri
A yau Talata 20 ga watan nan ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin, madam Hua Chunying ta yi Allah wadai da harin ta'addanci kan jakadan Rasha a Turkiya, tana mai cewa Sin na matukar kiyayya ga kowane irin nau'i na aikin ta'addanci. An ce, dan bindigar da ya gudanar da wannan danyen aiki dai ya yi hakan ne da nufin bayyana bacin ran sa game da matsayin Rasha a Syria.

Game da yadda wasu ke zargin Sin da Rasha kan hadin gwiwarsu game da batun Syria, madam Hua ta jaddada cewa, kasar Sin tana ganin cewa, karfafa mu'amala da hadin gwiwa tsakanin Sin da Rasha kan wasu muhimman harkokin duniya da na shiyya shiyya, zai sa kaimi ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a sassan. Kuma ta nanata cewa, Sin na goyon bayan kasa da kasa a kokarinsu na yaki da ta'addanci, tana kuma fatan za a karfafa hadin gwiwa da sauran bangarori daban daban a wannan fanni.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China