A yayin ganawar tasu, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, a yayin ganawarsa da shugaba Putin a taron hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" da aka gudanar a birnin Beijing, sun cimma matsaya game da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, gami da huldar abokantaka a tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare.
Haka kuma, ya ce, a halin yanzu, bunkasuwar dangantaka a tsakanin Sin da Rasha za ta ba da tabbaci ga ci gaban kasashen biyu da kuma kiyaye zaman karko na kasa da kasa, A saboda haka, akwai bukatar kasar Sin da kasar Rasha su nuna wa juna goyon baya don kare babbar moriyarsu, da inganta gudanar shawarar "ziri daya da hanya daya", domin cimma sakamako masu gamsarwa bisa hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu da kawancen tattalin arziki na Turai da Asiya, da zurfafa ma'amalar al'adu a tsakanin al'ummomin kasashen biyu da kuma yin hadin gwiwa yadda ya kamata cikin harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.
A nasa bangare shugaba Vladimir Putin ya ce, ci gaba da yin ma'amala a tsakanin shugabannin kasashen biyu yana da muhimmanci, domin fuskantar kalubalolin da harkokin kasashen duniya ke fuskanta. Ya kuma jaddada cewa, ya kamata a karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu wajen kiyaye zaman lafiya, da tsaro a duniya. (Maryam)