Rahotanni na cewa, kamfanonin kasar Afirka ta Kudu da kamfanin Zapper ne suka shigo da hidimar Alipay cikin kasar Afirka ta Kudu. A matsayin abokin hadin gwiwa na farko na Alipay, kamfanin Zapper ya samar da hidima a fannonin otel, sayar da kayayyaki, tikiti, ciniki ta intanet, bada kayayyaki kyauta, ajiye mota, biyan kudin makamashi da sauransu.
A ranar 27 ga watan Yuni ne, aka fara yin amfani da tsarin na Alipay karo na farko a kasar Afirka ta Kudu, inda aka yi amfani da tsarin wajen biyan tikitin bas na yawon shakatawa a kasar.
A halin yanzu, ana amfani da tsarin Alipay a kamfanoni fiye da dubu 200 a kasashe da yankuna 30 ciki har da kasashen Turai, da Amurka, da Japan, Koriya ta Kudu, kasashen yankin kudu maso gabashin Asiya, yankin Hongkong, yankin Macau, yankin Taiwan da sauransu, a fannonin da suka shafi abinci, kantuna yau da kullum, kantin sayar da kayayyaki da ba a biyan haraji, wuraren yawon shakatawa, filayen jiragen sama da sauransu. (Zainab Zhang)