Kakakin majalisar dokokin kasar Baleka Mbete, ya sanar da cewa 'yan majalisar 198 ne suka kada kuri'ar kin amincewa da kudurin tsige shugaban, yayin da 'yan majlisar 177 suka goyi bayan kudurin, 9 daga cikin 'yan majalisar kuma suka kauracewa kada kuri'ar.
'Yan majalisar dokokin na jam'iyyar ANC mai mulki sun kaure da shewa bayan da aka bayyana sakamakon.
Shugaban jam'iyyar Democractic Alliance Mmusi Maimane, ya bayyana cewa, za a cigaba da fafutukar tabbatar da ganin sun tumbuke Zuma daga mukaminsa. (Ahmad Fagam)