in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya jadadda muhimmancin shawo kan rikici a Afrika domin kare aukuwar yunwa
2017-10-13 09:44:28 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya jadadda muhimmancin shawo kan rikice-rikice a Afrika, domin magance abun dake sabbaba yunwa tun daga tushe a wasu kasashen nahiyar.

Antonio Guterres ya shaidawa kwamitin sulhu na majalisar a jiya cewa, duk da karin tallafin da ake samu daga al'ummomin kasashen waje, adadin wadanda ke cikin barazanar fadawa yunwa ya karu a kasashen Sudan da Somalia da Yemen da arewa maso gabashin Nijeriya.

Ya ce, mutane miliyan 6 ne ke fama da matsananciyar bukatar abinci a Sudan ta kudu, adadin ya kai miliyan 5 a farkon shekarar nan, yana mai cewa, agajin jin kai na ceton rayuka, amma kuma an gaza magance barkewar rikici wanda shi ne tushen dake haifar da yunwar.

Har ila yau, ya ce kaso 8 na kudin shirin samar da abinci na duniya na tafiya ne ga yankunan dake fama da rikici. Inda ya ce, kimanin kaso 60 daga cikin mutane miliyan 815 dake fama da yunwa na rayuwa ne a yankunan dake fama da rikici.

Ya ce, idan har ba a samar da maslaha ga rikice-rikicen, tare da samar da ci gaba ba, al'ummomi da baki dayan yankin za su ci gaba da fama da yunwa.

A don haka, Antonio Guterres ya yi kira ga bangarori masu rikici da juna a dukkan kasashen 4, su rugumi zaman lafiya, yana mai kira gare su su saukaka hanyoyin ba da agajin jin kai, tare da karewa da mutunta jami'an ba da agajin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China