Wakilin Hukumar FAO a Kenya Gabriel Rugalema, ya ce ingantattun dabaru da kara zuba kudi da amfanin da fasahohin zamani su ake bukata wajen bunkasa samar da abinci a kahon Afrika a lokcin da ake tsaka da fama da matsanancin yanayi.
Gabriel Rugalema na wannan jawabi ne yayin taro kan kawo karshen yunwa a yankin kahon Afrika, wanda ya samu halartar wakilan Gwamnatoci da na hukumomi da kuma masana.
A rahotonsa na baya-bayan nan, Ofishin MDD mai kula da ayyukan jin kai, ya yi kiyasin cewa mutane miliyan 26 ne ke fama da yunwa a yankin kahon Afrika.
Wakilin na FAO ya ce matsalar yanayi da dabarun ayyukan gona na dauri da rashin mai da hankali wajen tunkarar matsalar yanayi, su ne ke kawo tsaiko ga yunkurin ciyar da jama'a dake kara karuwa a yankin.
Ya kara da cewa, zamanantar da ayyukan gona tare da inganta muhimman abubuwa da suka hada da adanawa da rarrabawa da kuma sayar da amafanin gona, su ne jigo wajen kawo karshen yunwa a yankin.(Fa'iza Mustapha)