Mr.Wang Yi ya ce, Sin da kasashen Larabawa 'yan uwa ne, kana aminan juna ne. Sin na nuna yabo ga kasashen Larabawa bisa ga goyon bayan da suka ba ta kan batutuwan da suka shafi muradun kasar Sin da sauran muhimman al'amura, don haka, za ta ci gaba da kiyaye muradun kasashen Larabawa a batutuwan da ke jawo hankalinsu. Kasar Sin tana kuma son raba fasahohinta na samun ci gaban kasa tare da kasashen Larabawan.
A nasa bangare Mr.Gheit ya ce, kasashen Larabawa na dora muhimmanci sosai a kan bunkasa huldar da ke tsakaninsu da kasar Sin, kuma suna son hada kai da kasar Sin domin aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya.(Lubabatu)