in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Ya kamata kasa da kasa su kokarta don cimma burin MDD tare
2017-09-22 11:17:45 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce idan aka yi waiwaye, za a iya ganin babbar gudummawar da MDD ta bayar ga sha'anin zaman lafiya da ci gaban dan Adam, sai dai har yanzu ba a cimma burin Majalisar ba, a don haka, ya ce ya kamata kasa da kasa su ci gaba da yin namijin kokari wajen cimma wannan buri.

Wang Yi ya bayyana haka ne a jiya Alhamis, lokacin da yake jawabi ga babbar mahawarar da aka shirya yayin babban taron MDD karo na 72.

Baya ga wannan, Wang Yi ya nuna cewa, shekaru biyu da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taba yin kira a wajen irin wannan taro, inda ya ce kamata ya yi a kafa sabuwar dangankata tsakanin kasa da kasa da ke ba batun hadin kai don moriyar juna muhimmanci, domin samar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga bil Adama.

A cewar Ministan, wannan ra'ayi ya samu fahimta da amincewa sosai daga kasashen duniya, har ma ya zama burinsu baki daya.

Bugu da kari, Wang Yi ya yi nuni dacewa, ko da yaushe kasar Sin tana la'akari da burin jama'ar sauran kasashe a yayin da take kokarin cimma nata burin, za ta kuma taimakawa kasashen bisa ci gaban da ta samu, ta yadda za a samu ci gaba tare.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China