Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Rashan ta fitar, ta ce Amurka ce za ta dauki alhakin kara sukurkucewar dangantaka tsakanin sassan biyu, muddin dai ba ta dakatar da irin matakan da take dauka ba. Haka kuma a cewar tsagin Rashan, matakin na iya haifar da illa ga batun tsaro, da daidaito tsakanin sassan kasa da kasa.
A ranar Asabar din karshen mako ne dai jami'an Amurka suka rufe karamin ofishin jakadancin Rasha dake birnin San Francisco, da ofishin huldar cinikayyar kasar dake birnin Washington. Har wa yau an hana wakilan kasar ta Rasha shiga harabar ofishin kasar dake birnin New York. (Saminu Hassan)