Mista Pense ya isa Koriya ta Kudu a ranar 16 ga wata, a yayin da yake ziyara a yankin da ba na soja ba na kasashen Koriya ta Kudu da Koriya ta Arewa a ranar 17 ga wata, ya bayyana cewa, kasarsa ba za ta nuna hakuri ba kan Koriya ta Arewa.
Game da maganar Pense, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya bayyana a jiya cewa, idan kasar Amurka ta yi barazanar daukar matakan soja kan Koriya ta arewa bisa bangaren daya, to wannan zai kasance mataki mai hadari ne. Kasar Rasha ba ta amince da Koriya ta Arewa da ta taka kudurorin kwamitin sulhun MDD ba, don gudanar da ayyukan nazarin makaman nukiliya da yin gwajin makamai masu linzami, amma wannan ba ya nuna cewa, kasar Amurka ta iya taka dokokin kasa da kasa da tsarin mulkin MDD don daukar matakan soja. Kasar Rasha tana fatan Amurka ba za ta dauki mataki bisa bangaren daya kamar yadda ta yi kan kasar Syria a kwanan baya ba.
A nasa bangaren, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin mista Lu Kang, ya bayyana cewa, kasar Amurka muhimmin bangare ne dake shafar batun zirin Koriya, kasar Sin na maraba da Amurka da ta iya taka rawa kan warware batun zirin Koriya cikin lumana. (Bilkisu)