Yayin da yake zantawa da kafar yada labarun ABC a wannan rana, Herbert McMaster ya la'anci sabon gwajin harba makamai masu linzami da kasar Koriya ta arewa ta yi, a cewarsa wannan tsokana ce ta lalata zaman karko, ya kuma bayyana cewa, shugaba Donald Trump na kasarsa ya riga ya umurce kwamitin tsaron kasa da ya waiwayi kokarin da ma'aikatar tsaron kasa, ma'aikatar harkokin waje da kuma hukumomin tattara bayyanai na kasar suka yi wajen warware batun zirin Koriya, da nufin samar masa hanyoyin warware batun a lokacin da ya wajabta.
Baya ga haka, Herbert McMaster yana mai cewa, a cikin makwani har ma watanni masu zuwa, bangarori daban daban da batun ya shafa za su samu damar daukar matakai ban da amfani da karfin makamai don hana tabarbarewar halin. (Bilkisu)