Ita ma a nata bangaren, rundunar sojin Amurka ta sanar da cewa, binciken da ta yi ya nuna cewa, Koriya ta Arewa ta yi gwajin harba makamai masu linzami har sau uku da safiyar yau.
Har ila yau, rundunar sojan Koriya ta Kudu ta ce, an riga an gabatar da rahoto game da batun ga shugaban kasar Moon Jae-in, a waje daya kuma, tana ci gaba da yin nazari tare da takwararta ta Amurka kan al'amarin.
A halin yanzu, rundunonin sojoji na Koriya ta Kudu da Amurka na yin atisayen soja cikin hadin gwiwa a kasar Koriya ta Kudu.
Koriya ta Arewa dai ta yi Allah wadai da atisayen da sojojin ke yi, tana zargin lamarin da tsananta yanayin zaman dar-dar a zirin Koriya.
Bugu da kari, rahotanni na cewa, rundunar sojan yaki ta kasar Koriya ta Arewan ta yi gasar bajintar sojoji mai nufin mamaye tsibirai, karkashin jagorancin shugaban kasar Kim Jong-un. (Maryam)