Xi Jinping ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da takwaransa na Amurka Domald Trump ta wayar tarho.
Shugaba Xi ya bukaci bangarorin da abun ya shafa su kauracewa duk wani furuci ko wani mataki da ka iya ta'azzara zaman dar-dar da ake yi a zirin Koriya, ya na mai cewa a shirye Kasar Sin ta ke ta yi aiki da Amurka domin a warware matsalar yadda ya kamata.
Shugaba Xi ya jadadda cewa Kasar Sin da Amurka suna da manufa guda na rusa makaman nukiliya a zirin Koriya tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A nasa bangaren, shugaba Trump ya ce Amurka ta fahimci kokarin da kasar Sin ke yi na warware batun Nukiliyar, kuma a shirye ta ke ta ci gaba da tuntubar Sin akan manyan batutuwan kasashen ketare da na shiya-shiya da suka shafe su. (Fa'iza Mustapha)