Sabon kudurin kwamitin sulhu ya bayyana matsayin mambobinsa na bai daya, in ji kakakin kasar Sin
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a yau Litinin cewa, kuduri mai lamba 2371 da kwamitin sulhun MDD ya zartas a kwanan nan ya bayyana matsayin mambobin kwamitin na bai daya,har kullum kasar Sin na tsayawa kan daidaita batun zirin Koriya ta hanyar yin shawarwari.
A jiya ne kwamitin sulhu ya zartas da kuduri game da yadda kasar Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami a kwanan baya. Kakakin ya ce, kudurin ya dace da buri da ake fatan cimmawa na kiyaye zaman lafiyar shiyyar da kawar da makaman nukiliya daga shiyyar da kuma hana yaduwar makaman nukiliya a duniya baki daya.(Lubabatu)