Kasashen Sin da Amurka sun tattauna kan batun kulla yarjejeniyar shekara guda dangane da tattalin arziki a lokacin da bangarorin biyu suka yi wani taron musayar ra'ayoyi kan sha'anin tattalin arziki wato CED, a ranar Laraba.
Tattaunawar mai taken hadin gwiwar tattalin arzikin Sin da Amurka, an bayyana hakan ne cikin wata sanarwa daga wakilan bangaren kasar Sin mahalarta taron wanda aka gudanar na tsawon wuni guda.
A cewar sanarwar, kasashen biyu sun amince da yin hadin gwiwa a bangarorin bunkasa tattalin arziki, kudi, kasuwanci, zuba jari da kuma batun tafiyar da sha'anin tattalin arzikin duniya karkashin wani shiri na shekara guda.
Kasashen biyu, sun kuma amince za su yi aiki tare da juna domin shawo kan gibin kasuwanci dake tsakaninsu.
Dukkan sassan biyu za su kara fadada hadin gwiwa dake tsakaninsu game da batun ayyukan hidima da sha'anin masana'antu, da kara karfafa mu'amalar cinikayya da kayayyakin fasahar zamani.
Game da batun zuba jari, kasashen biyu za su kara fadada fannin zuba jarin cikin aminci da kuma samar da karin damammaki, da yin raba daidai, da gudanar da al'amurra a bude, da mayar da sassan biyun matsayin ingantattun wuraren zuba jari.
Dukkan bangarorin biyu za su karfafa batun tattalin arziki ta hanyar tuntubar juna da gudanar da al'amurra, tare da zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu game da dokokin da suka shafi kudi da bunkasuwar kasuwanni.(Ahmad Fagam)