Alkaluman baya-bayan nan da sashen baitul malin Amurka ya fitar na nuna cewa, kasar Sin ta ci gaba da rike matsayin kasa mai yawan takardun bashi a baitul malin Amuka sau hudu a jere.
A wayan Mayun wannan shekarar ce kasar Sin ta kara yawan takardun bashi na dala biliyan 10 da ta mallaka a baitul malin Amurkar, kuma halin yanzu tana da takardun bashin da suka tasamma dala triliyan 1,1022. Wasu bayanai da babban bankin kasar Sin ya fitar sun nuna cewa, a watan Yunin wannan shekara kudaden musayar kasar na ketare sun karu cikin watanni biyar a jere, alamun dake nuna cewa, kasar Sin za ta iya magance duk wata matsala da ta shafi batun hannayen jari.
Hukumar kula da kudaden musayar ketare ta majalisar gudanarwar kasar Sin, ta danganta karuwar kudaden musayar ketare da kasar ta samu a watan Yuni a kan yadda ake samun karuwar masu sha'awar zuba jari a cikin kasar, da karuwar darajar kadarori da ba ta shafi dalar Amurka ba.
Haka kuma takardun bashin kasar Japan, wadda ta sha gaban kasar Sin a watan Oktoban da ya gabata sun karu daga dala biliyan 4.4 zuwa dala triliyan 1,1113 a watan Mayun wannan shekara.
Ko da yake ya zuwa karshen watan Mayu, gaba daya takardun bashin kasashen ketare dake baitul malin Amurkar ya karu daga dala triliyan 6.0737 zuwa triliyan 6,1236 a watan Afrilun da ya gabata.(Ibrahim)