Mataimakin firaministan kasar Sin Wang Yang, ya yi kira ga Amurka da kasar Sin su hada gwiwa maimakon yin fito na fito, domin magance bambance-bambancen dake tsakaninsu.
Da yake jawabi yayin bude taro karon farko kan harkokin tattalin arziki tsakanin Amurka da Sin, Wang Yang, ya ce kasar Sin da Amurka manyan abokan cinikayya da zuba jari ne ga juna.
Ya ce, tattaunawa ba za ta kawo karshen matsalar nan take ba, amma kuma yin fito na fito ka iya lalata manufofin bangarorin biyu nan take.
Wang Yang ya kara da cewa, ba harkokin kasuwanci da al'ummomin kasashen ba ne kadai za su amfana da hadin gwiwar, har ma da duniya baki daya.
A cewar mataimakin firaministan, jigon tattaunawar ta yini daya shi ne, kara fahimtar juna da aminci da cimma matsaya guda.
Har ila yau, ya yi kira ga kasashen biyu, yana mai cewa, bisa kaskantar da kai da hangen nesa, bangarorin biyu su tabbata huldar harkokin tattalin arziki dake tsakaninsu ya samu tagomashi kan tafarkin da ya dace tare da samar da sakamako masu kyau.
Wang Yang ya ce, a shirye kasar Sin take ta yi aiki da Amurka domin cimma nasararorin da bangarorin biyu za su amfana da su.(Fa'iza Mustapha)