Michael Moller, darakta janar na ofishin MDD a Geneva, shi ne ya gabatar da jawabin na mista Guterres a lokacin bikin wanda ya samu halartar muhimman mutane a fadin duniya da kasar Afrika ta kudu, inda jama'in MDDr ya bayyana wasu hikimomin da Mandela ke da su da suka hada da tausayi da kaunar dan adam.
Duniya zata dade tana tunawa da Nelson Mandela sakamakon babban misali da ya nuna na sadaukar da kai da yin aiki tukuru domin tabbatar da adalci da samar da 'yancin dan adam da zaman lafiya.
Ranar 18 ga watan Yuli ita ce ranar da MDD ta kebe domin tunawa da haihuwar Mandela, shi ne shugaban Afrika ta kudu na farko da mafi yawan 'yan kasar suka amince da jagorancinsa, kuma gwagwarmayar da ya gudanar na yaki da wariyar launin fata da ceto al'umma ya ba shi damar shiga cikin jerin mutane mafiya daraja a duniya a karni na 20.
Moller yace, Nelson Mandela ya kasance mutum mai baiwa muhimmanci ga fannin ilmi da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa, da yaki da nuna wariya da kuma bada gudunmowa wajen cigaban dan adam da yaki da talauci, inda jami'in ya bukaci a yi koyi da rayuwarsa don inganta jin dadin rayuwar bil adama.(Ahmad Fagam)