Kaza lika yayin taron, an tattauna game da hanyoyin inganta rayuwar al'ummun wannan yanki, wadanda da yawa ke rasa muhallan su sakamakon rigingimu iri daban daban.
Dandalin samar da ci gaba da bunkasa harkokin cinikayya na MDD ko UNCTAD a takice, da hadin gwiwar ofishin wakilin musamman na babban magatakardar MDD game da yankin manyan tafkunan na Afirka ne suka shirya taron a jiya Talata.
Cikin mahalarta taron dai hadda babban sakataren UNCTAD Mukhisa Kituyi, da mataimaki na samuamman ga babban magatakardar MDD Said Djinnit. Wadannan jami'ai biyu sun tabo batu game da matakan da taron birnin Geneva ya zayyana na bunkasa hada hadar cinikayya, da ma irin tasirin su, warware matsaloli masu sarkakiya da al'ummun sassan duniya ke fuskanta.
Da yake tsokaci game da hakan Mr. Mukhisa Kituyi, ya ce yankin tafkunan Afirka na da sama da mutane miliyan 7, wadanda ke rasa muhallansu, da kuma 'yan gudun hijira kusan miliyan 3.5.
A nasa bangare kuwa, Mr. Said Djinnit, cewa ya yi ya zama wajibi, a gwama matakan siyasa da sauran dabaru, domin dawo da wannan yanki cikin hayyacin sa. (Saminu)