An bukaci da a aiwatar da yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci tsakanin yankuna uku na kasashen Afrika cikin sauri, a cewar sakamakon taron majalissar ministocin ciniki bai daya ga gabashin da kudancin Afrika COMESA da aka fitar a ranar Litinin din nan.
An kaddamar da shirin ciniki cikin 'yanci tsakanin yankunan uku dai COMESA da kungiyar kasashen gabashin Afrika EAC, da kuma kungiyar ci gaban kasashen kudancin Afrika SADC a watan Yunin bana a kasar Masar.
Amma ita majalissar ministocin kungiyar COMESA ta bayyana shakkunta cewar, akwai yawan kasashen da ba su rattaba hannu a kan yarjejeniyar ba, sannan kuma wadanda suka rattaba ba su tabbatar da hakan bisa doka ba.
Majalissar ministocin ta bukaci mambobi kasashe da suka rattaba hannu a cikin yarjejeniyar yankunan uku wato COMESA-EAC-SADC na ciniki cikin 'yanci da su fara aiwatar da ita, kuma ta bukaci wadanda ba su rattaba hannu ba su yi hakan, in ji ministocin a cikin sanarwa bayan taro da aka fitar a Lusaka, babban birnin kasar Zambiya.
A cewar sanarwar, 16 daga cikin 26 na kasashe a yankunan uku na nahiyar sun rattaba hannu a yarjejeniyar, amma ba su tabbatar da ita bisa doka ba.
Bayan yaba wa da ci gaban da aka samu, ministocin sun bukaci mambobi kasashe da su tabbatar da an kammala sauran batutuwa, tare da samar da hanyoyi mafiya sassauci ga 'yan kasuwa domin a samu tafiyar da ciniki da zuba jari a tsakanin kan iyakoki.(Fatimah)