in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afirka na neman a kafa yankin cinikiyya maras shinge a nahiyar
2016-07-20 10:47:42 cri

Ministocin harkokin cinikayya na kasashen Afirka sun bukaci taron cinikayya da ci gaba na MDD(UNCTAD) da ya taimakawa kokarin da gwamnatocin kasashen ke yi wajen ganin sun samu kudaden tafiyar da harkokin cinikayya da kuma tattaunawa, ta yadda za a kafa yankin yarjejeniyar cinikayya maras shinge a nahiyar Afirka(CFTA).

Ministan cinikayya da masana'antu na kasar Afirka ta kudu Rob Davies wanda ya bayyana hakan a yayin wannan taro ya ce, kasashen Afirka suna bukatar kungiyoyin kudi na kasa da kasa, kamar bankin duniya da bankin raya Afirka da sauran bankuna da ke shiyyar, da su zuba jari a bangaren masana'antun samar da kayayyaki, ta yadda kasashen Afirka za su samar da isassun kayayyakin da za su fitar zuwa kasashen ketare.

Ita ma kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta yi kiran da a kafa wannan yanki nan zuwa shekarar 2017, ta yadda zai taimakawa kasashen na Afirka ninka harkokinsu na cinikayya da zuba jari, a matsayin matakin farko na karfafa dunkulewar shiyyar.

A nasa jawabin, ministan cinikayya na Najeriya Okechukwu Enelamah ya ce, kasashen Afirka na bukatar nagartattun manufofi da za su bunkasa kayayyakin da suke samarwa a cikin gida, matakin da ministan ya ce shi ne ginshikin ci gaba da kuma kawar da talauci a cikin kasa.

Kasashen na Afirka dai sun bukaci dandalin na UNCTAD da ya yi kokarin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a taron kungiyar cinikayya ta duniya (WTO).(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China