Bisa alkaluman da hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar, an ce daga watan Janairu zuwa watan Maya na bana, jimillar kudin shige da fice a tsakanin Sin da kasashen Afirka ta kai dala biliyan 70.14, adadin da ya karu da kashi 22.2 cikin dari bisa na makamancin lokaci a bara.
Cikin wannan adadi, kudin da aka samu daga safarar kaya zuwa Afirka ya kai dala biliyan 38.29, adadin da ya karu da kashi 7 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara, yayin da adadin kudin da aka samu a fannin shigo da kaya daga nahiyar Afirka ya kai dala biliyan 31.85, wanda shi ma ya karu da kashi 47.8 cikin dari. (Kande Gao)