in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AWF ta yabawa matakin kasar Sin na hana fataucin haurin giwa
2017-01-19 09:53:19 cri

Kungiyar kare namun daji ta Afirka AWF ta yabawa matakan da mahukuntan kasar Sin suka dauka na hana sarrafawa da cinikin hauren giwa ya zuwa karshen shekarar 2017.

Shugaban kungiyar Kaddu Sebunya, wanda ya bayyana haka a birnin Nairobin kasar Kenya, ya ce wannan mataki na kasar Sin zai taimaka wajen kawo karshen farautar namun daji da sauran ayyukan da ke barazana ga giwaye a nahiyar Afirka.

Sebunya ya ce, muddin aka yi nasarar rufe kasuwannin sayar da haurin giwa, hakan zai taimaka wajen kawo karshen barazanar da muhimman namun daji kamar giwaye da karkanda suke fuskanta a doron kasa.

Bayanai na nuna cewa, yanzu haka hukumomin kasa da kasa sun hada kai da gwamnatocin Afirka da masu kare namun daji, da nufin bullo da matakan yaki da cinikin haurin giwa a Afirka.

A watan Disamban shekarar 2016 ne mahukuntan kasar ta Sin suka samar da haramta ciniki da sarrafa haurin giwa, a wani mataki na cika alkawarin da ta yi na taimakawa kokarin da kasashen duniya suke yi na yaki da masu farautar namun daji.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China