in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Kenya za su zurfafa hadin gwiwa wajen kare tsirrai
2017-05-16 09:43:06 cri

Kasar Sin za ta zurfafa hadin gwiwa da kasar Kenya a sha'anin binciken kimiyya domin kiyaye ci gaban fannin gandun daji a kasar ta gabashin Afrika.

Wang Qingfeng, daraktan cibiyar bincike ta Sin da Afrika (SAJOREC) wadda reshe ce ta cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin ya tabbatar da cewa, Sin a shirye take ta tallafawa Kenya wajen inganta albarkatun tsirrai a kasar.

Wang ya ce, a shekaru 5 da suka gabata, wato bayan da suka sanya hannu kan yarjejeniya da hukumar kula da wuraren adana kayayyakinn tarihi ta kasar Kenya (NMK), sun kara zurfafa hadin gwiwa wajen gudanar da bincike don inganta fannin shuke shuke domin bunkasa fannin gandun daji.

Wang ya furta hakan ne a yayin zantawa da kamfanin dillancin labaran Xinhua a lokacin wani taro na kungiyar nazarin tsirrai ta Afrika wato (AETFAT) karo na 21, wanda aka gudanar a Nairobi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China