Sanarwar da Ministan harkokin wajen Sin Lu Kang ya fitar yau Jumma'a, ta ce shugaban Xi zai kai ziyarar ne bisa gayyatar da Shugaban Kazakhstan Nursultan Nazarbayev ya yi masa.
Shugaba Xi zai kuma halarci taron majalisar gudanrwar shugabannin kasashen kungiyar kawance ta Shanghai SCO da kuma bikin bude baje kolin duniya a Astana. (Fa'iza Mustapha)