Shugabannin biyu sun jinjinawa nasarorin da aka samu, wajen raya huldar dake tsakanin kasashensu, bayan da suka kulla dangantakar jakadanci shekaru 25 da suka gabata, inda kuma suka tattauna kan fannoni da bangarorin da za su yi hadin-gwiwa kan su a nan gaba. Shugabannin biyu sun kuduri aniyar kara habaka dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa tsakaninsu, ta yadda al'ummar Sin da Kazakhstan za su ci gajiyar hakan. (Murtala Zhang)