A wannan rana, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wani kuduri, inda ya yi allah wadai da kakkausar murya kan gwajin makamai masu linzami da kasar Koriya ta Arewa ta yi, sa'an nan, an shigar da karin mutane da kamfanonin da abin ya shafa cikin jerin wadanda za a kakaba musu takunkumi.
A yayin taron, Liu Jieyi ya ce, ana fuskantar matsaloli da dama game da yanayin zirin Koriya, kuma a halin yanzu, ana cikin wani muhimmin lokaci ganin bangarorin daban daban da batun nukiliyar kasar Koriya ta Arewa ya shafa teburin sun koma ga yin shawarwari.
Bugu da kari, ya ce, ya kamata bangarorin da abin ya shafa su kai zuciya nesa, domin sassauta yanayin tashin hankali da ake ciki, lamarin da zai ba da gudummawa wajen karfafa fahimtar juna a tsakaninsu. (Maryam)