Kwanan baya, bankin duniya ya bayyana cewa, bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara za ta sake samun raguwa a shekarar 2016, zuwa wani adadi na kashi 1,6 cikin 100. Wannan ja da baya cikin sauri na bunkasuwar daga dukkan fannoni ya faru ne bisa dalilin yanayin matsalolin tattalin arziki da suke fuskanta, amma sauran kasashe kamar su Habasha da Rwanda da Tanzaniya suke ci gaba da samun wani adadin bunkasuwa na shekara da ya zarce kashi 6 cikin 100. (Maman Ada)